Mutane Biyu Sun Mutu Sakamakon Cutar Lassa Fever A Jihar Benue

Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Benue ta sanar da mutuwar mutane biyu sakamakon kamuwa da cutar Lassa fever a jihar.

Kwamishinan Lafiya da Ayyukan Jinƙai, Dakta Paul Ogwuche, ya ce barkewar cutar ta fara ne cikin makonni biyu da suka gabata.

A cewarsa, mutane tara ne ake zargin sun kamu da cutar, inda biyar daga cikinsu suka tabbatar da kamuwa da ita.

Daga cikin waɗanda suka kamu, akwai ma’aikatan lafiya biyu, lamarin da ya ƙara tayar da hankula.

Kananan hukumomin Makurdi da Buruku ne suka fi fama da cutar, duk da cewa wasu marasa lafiyar an gano su ne a Makurdi.

Gwamnati ta wakilta tawaga ta gaggawa tare da ƙara wayar da kan jama’a kan hanyoyin kauce wa kamuwa da cutar.

Kazalika su kula da tsafta, su guji hulɗa da beraye, tare da hanzarta neman magani idan aka ga alamomin Lassa fever.

Comments (0)
Add Comment