Nasir Charity Development Foundation (NANAS) sun aurar da mata 300 a garin Birnin Kebbi

Gwamnatin jihar Kebbi karkashin jagorancin Gwamna Nasir Idris tare da hadin gwiwar gidauniyar Nafisa Nasir Charity Development Foundation (NANAS) sun aurar da mata 300 a garin Birnin Kebbi tare da shawartar ma’auratan da su kasance masu sada zumunci da son juna.

Bikin wanda ya gudana a fadar Mai Martaba Sarkin Gwandu, Gidauniyar NANAS ce ta shirya, wanda matar Gwamnan, Hajiya Nafisa Nasir Idris ta kafa.

Da take jawabi a wajen bikin mai dakin gwamnan jihar tace, an gudanar da auren ne a wani yunkuri na rage yawan zawarawa da kuma mace-macen aure a cikin al’umma.

Kakakin majalisar dokokin jihar Hon. Muhammad Usman Ankwe, shine ya wakilci gwamna a wajen bikin daurin auren, inda ya bayyana cewa, za’a gudanar da irin wannan daurin auren lokaci-lokaci domin taimakawa marasa galihu maza da mata. Dakta Nasir Idris ya ce, gwamnatinsa ta bayar da jimillar Naira miliyan 21 a matsayin sadaki ga matan da aka daura wa aure 300 da suka fito daga kananan hukumomin jihar 21, inda kowace amarya za ta samu sadaki Naira 70,000.

Comments (0)
Add Comment