Rarara Ya Bukaci Kotu Da Tayi Watsi Da Karar Sa Da Aka Shigar Gabanta

Fitaccen mawakin siyasar jihar Kano, Dauda Kahutu Rarara, ya bukaci wata babbar kotun shari’ar Musulunci ta jihar da ta yi watsi da karar da aka shigar a gabanta.
Ana tuhumar Dauda Rarara da rashin biyan kudi sama da naira miliyan 10 ga wani dan kasuwa, Muhammad Ma’aji.
A zaman da kotun dake zama a Rijiyar Zaki karkashin jagorancin mai shari’a Halhalatul Khuza’i Zakariyya, lauyan Dauda Rarara ya shaida wa kotun cewa shari’ar ba ta da tushe don haka a yi watsi da ita.
Ya kara da cewa sun bayar da amsarsu a rubuce ga mai kara da kotu, amma masu gabatar da kara sun yi ikirarin cewa sun samu a makare a lokacin da kotu za ta zauna.
Wanda ya shigar da karar, Muhammad Ma’aji, ya shaida wa kotun cewa yana da dukkan shaida a rubuce domin tabbatar da ikirarin nasa tun farkon dangantakarsa kasuwancinsa da Dauda Rarara a shekarar 2021 amma bai biya shi ko sisi ba.
Alkalin kotun ya dage sauraron karar zuwa ranar 12 ga watan Mayu domin ci gaba da sauraro.

Comments (0)
Add Comment