Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya lalata wani bangare na cibiyar lafiya ta garin Saleri dake yankin karamar Hukumar Kirikasamma anan jihar Jigawa.
Manajan Hukumar lafiya matakin farko na yankin Usman Abdullahi Birniwa ya sanar da hakan ga manema labarai a Birniwa.
Yace ruwan saman hade da iska ya lalata sashen kula da mata masu juna biyu da kuma wasu kayayyakin aiki.
- Kasar Turkiyya ta dakatar da duk wata hulɗar kasuwanci da Isra’ila
- An shawarci al’ummar jihar Jigawa su tashi tsaye wajen dasa bishiyoyi da renon su
- Ministan ma’aikatar albarkatun ruwa da tsaftar muhalli ya kaddamar da cibiyar samar da ruwan sha dake garin Birnin Kudu
- Gwamnatin tarayya ta bayyana shirinta na sake duba farashin lasisin hakar ma’adanai
- Sauye-sauyen tattalin arzikin da shugaba Bola Tinubu yayi ne ya fardado da Najeriya daga durkushewa
Usman Abdullahi yace a yanzu haka ambaliyar ruwa na neman mamaye cibiyar lafiyar inda ya roki gwamnati data kai musu daukin gaggawa.
Tunda farko kamsilan sashen tsare tsare Abdullahi Gada yace karamar hukumar ta bada gudunmawar fatun bahuna 200 domin yin jinga a cibiyar.
Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje 46 yayin da kayayyakin amfanin gona na miliyoyin naira suka salwanta a garin na Saleri.