Ofishin hukumar hana safarar mutane ta kasa na shiyyar Kano ya kama wasu mutane uku a Kano bisa zargin sayar da wani yaro dan shekara daya a jihar Imo.
Wadanda ake zargin sune kwamandan Hisbah na Fagge, Jamilu Mohammed, da dagacin Fagge, tare da wata mata mai suna Loveth wacce ta sayi yaron.
Shugaban ofishin shiyyar, Shehu Umar, ya gayawa manema labarai cewa an gayyaci wadanda ake zargin domin amsa tambayoyi dangane da lamarin.
- Gwamnatin Sokoto Ta Bai Wa Sojojin Najeriya Gudummuwar Motocin Sulke 62
- Guguwar Iska Ta Kashe Mutane Uku, Ta Lalata Gidaje Da Ababen More Rayuwa A Yobe
- Sojoji Sun Kashe ‘Yan Ta’adda Takwas, Sun Kwato Makamai A Katsina
- Gwamnan Zamfara: Na Ƙi Biyan Kuɗin Fansa Naira Miliyan 300, Na Ce Su Kashe ‘Yan Uwana
- EFCC Ta Gurfanar da Bello Bodejo Kan Zargin Badaƙalar Kuɗi
An gano cewa yaron da aka sayar, iyayensa ne suka jefar da shi, kuma ake kula da shi a hukumar Hisbah.
Sai dai, an zargin kwamandan Hisbah ya hada baki da dagacin inda suka sayar da shi. A cewar shugaban hukumar, yaron wanda ake zargin kwamandan Hisbah tare da dagacin Fagge sun sayar da shi ga Loveth, an ceto shi daga hannun mahaifiyar Loveth a jihar Imo.