SEMA ta bayyana shirinta na sayen karin kayan agaji domin taimakawa jama’a a lokacin damina – JIGAWA

Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Jigawa (SEMA) ta bayyana shirinta na sayen karin kayan agaji domin taimakawa jama’a a lokacin damina, kamar yadda sabon Sakataren hukumar, Alhaji Hannafi Yakubu Fagam, ya bayyana a wata tattaunawa da akayi da shi a Radio Jigawa a cikin wani shiri mai suna Jigawa A Yau.

Ya ce za’a sayi kayan da suka hada da jarkokin mai, garin fulawa, sukari, kwale-kwale, garin kwari, bargo, tabarma da sauran kayayyakin kariya don rage illar ambaliya.

Hannafi Fagam ya kara da cewa za a horar da ma’aikatan kananan hukumomi don kara fahimtar dabarun daukar matakan gaggawa a lokacin ambaliya. Ya ce hukumar ta rubuta littafi mai dauke da tsare-tsare da matakan kariya daga ambaliya, inda ya kara da cewa hukumar NiMet na hasashen cewa za a samu ruwan sama mai yawa a jihohi da dama, ciki har da jihar Jigawa, musamman a kananan hukumomi kamar Ringim da Taura da Jahun da Miga da Kafin Hausa da Auyo da Hadejia da Kirikasamma da Guri da Malam Madori da kuma Kaugama.

Comments (0)
Add Comment