Shugaba Buhari ya umarci sojojin Najeriya da su yi amfani da karfi wajen murkushe yan bindigar

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umarci sojojin kasarnan da su yi amfani da karfi wajen murkushe ’yan bindigar da ke kashe-kashe da garkuwa da mutane a Jihar Neja.

Wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu ya fitar a jiya ta ce shugaban kasar ya bayar da umarnin ne ga helkwatar Tsaro ta Kasa.

Shugaba Buhari ya nanata cewa samar da tsaro nauyi ne da ya rataya a wuyan kowace al’umma kuma ta hanyar bai wa hukumomin tsaro hadin kai ne za a iya kawo karshen matsalolin tsaro da suka addabi kasarnan.

Comments (0)
Add Comment