Shugaba Buhari ya yi alkawarin yin duk mai yiwuwa don magance matsalolin tsaro da kasar Najeriya ke fuskanta

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawarin yin duk mai yiwuwa don magance matsalolin tsaro da kasarnan ke fuskanta, inda ya bayyana fatansa na gudun barin gwamnati a matsayin wanda ya gaza.

Shugaba Buhari ya yi alkawarin a jiya yayin taron majalisar tsaro ta kasa a Fadar Shugaban Kasa dake Abuja.

Mai bayar da shawara kan harkokin tsaro na kasa, Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya, wanda ya yiwa manema labarai bayani a fadar shugaban kasa bayan taron, ya ce Shugaban kasar ya nuna farin cikinsa kan nasarorin da hukumomin tsaro suka samu zuwa yanzu a yakin da ake yi da masu tayar da kayar baya, da ‘yan fashin daji, da masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata laifuka a sassa daban-daban na kasarnan.

Monguno ya ce Shugaban kasar ya kuma nuna a shirye yake ya yi wasu sauye-sauye a tsarin tsaro na kasarnan, idan hakan ya zama dole.

Comments (0)
Add Comment