Wani Direban Mota Ya Kashe ‘Yan Gida Daya Su Hudu Har Lahira A Jihar Jigawa

Wani direban motar haya ya kashe ‘yan gida daya su hudu har lahira a karamar hukumar Babura ta jihar Jigawa.

Wani mazaunin garin ya shaida wa manema labarai cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Lahadi inda wata mota ta bugi babur din da ke dauke da wadanda abin ya rutsa da su, inda duk suka mutu nan take.

Kakakin hukumar tsaron fararen hula civil defence a jihar Jigawa, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai.

A cewar sanarwar, lamarin ya faru ne a lokacin da direban motar hayar mai suna Hamisu Ahmed da ke tafiya zuwa Gumel yana tuki a guje ya afkawa wadanda lamarin ya rutsa da su dake kan babur a hanyarsu ta kauyensu Kolori.

Sanarwar ta kara da cewa, wadanda aka kashen sun hada da Gambo Mutari mai shekaru 45 da matarsa Fiddausi Abdullah mai shekaru 25 da kuma surukarsa Hauwa Maigari da dansa mai shekaru biyu.

An garzaya da su zuwa babban asibitin Babura inda aka tabbatar da rasuwarsa.

Comments (0)
Add Comment