Wasu rahotanni da suke fitowa daga Kasar Sudan na cewa an yi juyin mulki a kasar.
sannan an kama mambobin gwamnatin rikon kwarya a kasar.
Fira ministan kasar Abdallah Hamdok, da wasu ministoci hudu na daga cikin wadanda aka yi amanna cewa wasu sojoji da ba a tantance ko su waye ba sun kama tare da tsare su a safiyar yau Litinin.
Sojoji dai basu ce komai ba kawo yanzu game da juyin mulkin.
Wata sanarwa daga ma’aikatar yada labaran kasar ta wallafa a shafinta na Facebook cewa wata hadakar rundunar sojojin kasarce ta kama fira ministan da ministocin hudu in da ake tsare da su a wajen da ba a bayyana ba.
Rahotanni sun ce an katse layukan sadarwa a kasar.
Sannan, an bada rahoton cafke mai bai wa mista Hamdok shawara kan harkokin yada labarai.
Tuni Kungiyar kwararru a Sudan sun yi kira ga jama’a da su fito kan tituna domin nuna bijirewa juyin mulki.