Wata zanga-zanga ta barke yau a Jibiyan jihar Katsina, bisa kisan wasu mutane 5 da jami’an kwastan suka yi lokacin da suke kokarin kama masu fasa kwaurin shinkafa a yankin.
Shaidun gani da ido sun ce wasu dayawa daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su, sun samu raunuka kuma suna karbar magani a wani karamin asibiti.
Shaidun sun ce motar jami’an kwastan ta bi ta kan wani gungun mutane, a lokacin da suke gudu a kokarinsu na kama masu fasa kwaurin shinkafa, inda suka kashe mutane 5 tare da jikkata wasu da dama.
Kakakin yansandan jihar Katsina, Gambo Isah, bai amsa kiran wayarsa ba domin magana akan lamarin.
Sai dai, jami’in hulda da jama’a na hukumar kwastan a jihar Katsina, Danbaba Isah, ya musanta cewa jami’an hukumar suna bin sahun wata mota ne.
Danbaba Isa yayi kira ga jama’a da su kauracewa yada labaran da basu tabbatar ba.