Yadda aka sace tsohon dan majalisar dokokin jihar Jigawa

An sace wani tsohon dan majalisar dokokin jihar Jigawa, Haladu Bako.

Mansur Ahmed, hadimin tsohon gwamnan Jigawa, Sule Lamido, ya ce an sace Haladu Bako ne a daren jiya yayin da yake tafiya daga Kano zuwa jihar Jigawa.

Mansur Ahmed ya tunatar da cewa Haladu Bako ya wakilci karamar hukumar Auyo a majalisar dokokin jiharnan daga shekarar 2007 zuwa 2015.

Haladu Bako, jigo a jam’iyyar PDP a jihar Jigawa, ya sake tsayawa takara amma ya rasa kujerar a zaben shekarar 2019.

Lokacin da aka tuntubi kakakin ‘yan sandan Jihar Jigawa, Lawan Shisu Adam ya ce har yanzu ba shi da labarin abin da ya faru.

Ba a fiye samun matsalar satar mutane domin neman kudin ba a nan jihar Jigawa.

Sai dai, manazarta sun yi gargadin cewa tabarbarewar rashin tsaro da ke faruwa a yankin Arewa maso Yamma na iya jawo matsalar zuwa jiharnan.

Comments (0)
Add Comment