Yadda wata ‘yarjarida ta yi karuwancin watanni bakwai don samun labari

Wata ‘yarjarida mai binciken kwakwaf da ke tarayar Nijeriya Tobore Ovuorie ta ci lambar yabo ta DW na wannan shekarar 2021 a dai dai lokacin da ake bikin ranar’yanjarida ta duniya.

Tobore Ovuorie, tana cikin manyan ‘yanjarida masu binciken kwakwaf da bin diddigi a kasar, da take da burin tsage gaskiya da kuma bankado boyayyun al’amura.

Majiyar gidan jaridar DCL Hausa tace a shekarar 2013, ta yi kasadar shiga aikin karuwanci na tsawon watanni 7 dan bankado yadda ake safarar mata domin karuwanci da kuma sayar da sassan jikin bil’adama.

Jaridakaruwanci
Comments (0)
Add Comment