Wata ‘yarjarida mai binciken kwakwaf da ke tarayar Nijeriya Tobore Ovuorie ta ci lambar yabo ta DW na wannan shekarar 2021 a dai dai lokacin da ake bikin ranar’yanjarida ta duniya.

Tobore Ovuorie, tana cikin manyan ‘yanjarida masu binciken kwakwaf da bin diddigi a kasar, da take da burin tsage gaskiya da kuma bankado boyayyun al’amura.

Majiyar gidan jaridar DCL Hausa tace a shekarar 2013, ta yi kasadar shiga aikin karuwanci na tsawon watanni 7 dan bankado yadda ake safarar mata domin karuwanci da kuma sayar da sassan jikin bil’adama.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: