Jagoran jam’iyyar APC a Najeriya kuma tsohon gwamnan jihar Lagos, Bola Tinubu, ya yi gargadin cewa kasar za ta iya fuskantar wani sabon yaki idan ta wargaje.

Da yake jawabi a wurin lacca da gwamnatin jihar Lagos ta hada a kan azumin Ramadan ranar Lahadi, Tinubu ya ce Najeriya za ta fi dorewa idan tana dunkule wuri daya.

Yana yin wannan jan hankali ne a yayin da wasu ‘yan kasar musamman ‘yan IPOB ke fafutukat ballewa daga Najeriya, inda suke matsa kaimi wajen kai hare-hare kan ‘yan sanda da wasu hukumomin gwamnati a yankin kudu maso gabashin kasar.

Sai dai Tinubu ya ce “ba za mu amince” Najeriya ta balle ba yana mai cewa ba shi da kasar da zai je idan kasar ta wargaje.

Tsohon gwamnan na jihar Lagos ya kara da cewa kasar ba za ta yi ganganci sake fadawa yaki ba saboda har yanzu tana ci gaba da shan wahala sakamakon illar da yakin basasa ya yi mata.

“Allah ba zai bar Najeriya ta sake shiga yaki ba. Idan muka ce Najeriya ta rabu, ya kamata mutane su tuna abin da yaki ya haifar a Sudan da Iraki,” in ji shi.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: