Tarar N100,000 za aci kan duk wanda ya sare bishiya

0 129

Hukumar Babban Birnin Tarayya Abuja ta ce daga yanzu duk wanda aka samu da laifin sare bishiya zai biya tarar N100,000.

Hukumar ta bayyana haka ne a sakon da ta wallafa a shafinta na Twitter ranar Litinin.

Sanarwar ta ambato Daraktar kula da wuraren shakatawa, Mrs Riskatu Abdulazeez, tana kara da cewa “haramun ne sare bishiyoyin da aka dasa a cikin gidajen jama’a ba tare da neman izinin gwamnati ba.”

A cewarta sare bishiyoyin na ta’azzara matsalolin da ke da dangantaka da sauyin yanayi don haka ba za su bari mazauna birnin su ci gaba da sare bishiyoyi ba tare da la’akari da illar yin hakan ba.

“Duk wanda ya sare bishiya ba bisa ka’ida ba zai biya tarar N100,000 kuma za a tilasta masa dasa sabbin bishiyoyi biyu domin maye gurbin wacce ya sare.” in ji Mrs Riskatu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: