‘Yansanda sun kama wasu matasa uku da ake zargi da garkuwa da mutane a Hadejia

Rundunar ‘yansanda jihar Jigawa ta kama wasu matasa uku da ake zargi da garkuwa da mutane a yankin karamar hukumar Hadejia.

Kakakin rundunar, Lawan Shiisu, cikin wata sanarwar da ya fitar jiya a Dutse yace an kama wadanda ake zargin bayan an zarge su da kokarin yin garkuwa da wani mutum mai suna Cyprian Okechukuw a ranar 31 ga watan Mayu.

Yayi bayanin cewa wadanda ake zargin sun yi sojan gona a matsayin jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi (NDLEA) inda suka yi yunkurin dauke mutumin.

A cewarsa, jami’an yansanda sun kwace wata karamar bindiga kirar hannu daga wajen wadanda ake zargin.

Shiishu Adam yace wadanda ake zargin su uku da suka hada da Mujahid Muhammad dan shekara 30 da Shahid Ibrahim mai shekara 20 da Haidar Muhammad Kabir dan shekara 23, dukkansu yan unguwar GRA a nan Hadejia, daga baya an kama su bayan bincike da aka bayyana kamanninsu.

Kakakin na yansanda yace ana cigaba da bincike kan lamarin kuma ana kokarin ganowa da kama sauran wadanda ake zargi.

Comments (0)
Add Comment