Za a daga likkafar makarantar koyar da fasahar sadarwa ta zamani dake Kazaure zuwa polytechnic ta fasahar sadarwa

Za a daga likkafar makarantar koyar da fasahar sadarwa ta zamani dake Kazaure zuwa polytechnic ta fasahar sadarwa.

Shugaban makarantar Farfesa Babawuro Usman ya sanar da hakan ta cikin wani shirin Radio Jigawa.

Yace daga likkafar makarantar zuwa polytechnic ta fasahar sadarwa zai bata damar samun dama da yawa da suka hadar da Karin kwasa kwasai da samun tallafin asusun bunkasa ilmi na kasa da sauransu.

Farfesa Babawuro Usman ya kara da cewar tuni gwamnati ta yi kasafin kudi kan hakan domin kara samun bunkasa koyo da koyarwa a makarantar.

Yace sun aiwatar da dukkannin tanade tanaden kasafin kudin 2021 na makarantar yayinda suka gudanar da manyan aiyuka guda tara da suke cikin kasafin kudin na bara.

Daga nan sai ya bukaci hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta kasa NITDA da kuma hukumar sadarwa ta kasa da su tallafawa makarantar kamar yadda suka nema a bara.

Comments (0)
Add Comment