Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya amince da cewa miliyoyin ‘yan Najeriya na fama da bakin talauci.
Yace shugabannin da aka zaba a yanzu, zasu zama na jeka na yi ka matukar basu hada kai ba wajen magance abinda da ya kira matsalolin dake neman tarwatsa kasarnan ba.
Osinbajo ya fadi hakan ne yayin bikin rufe taron wuni biyu tsakanin bangaren zartarwa da majalisa wanda aka gudanar a fadar shugaban kasa dake Abuja.
- Gwamnatin Gombe Ta Ware N260m Don Sauya Wa Kasuwar Hatsi Matsuguni
- TUC Za Ta Karfafa Haɗin Gwiwa da Gwamnatin Jigawa Don Walwalar Ma’aikata
- Mutum 3,000 Sun Yi Hijira Saboda Hare-Haren ’Yan Bindiga A Katsina
- An Kama Jami’in DSS Na Bogi A Abuja
- Davido Aka So Kashewa A Harin da Aka Kai Wa Tawagar Adeleke — ’Yan Sanda
Yace akwai bukatar yan bangaren zartarwa da yan majalisa su hada kai muddin suna gudun bawa yan Najeriya kunya, wadanda suka basu damar rike mukaman siyasa a manyan matakai.
A takardar bayan taro da aka fitar a karshe taron, wadanda suka halarci taron, sun nemi a samar da shiri mai inganci na sansanta juna tsakanin bangaren zartarwa da na majalisa, domin cigaban kasa.