Al’ummar Kano Ba Su Tare da Kalaman Sheikh Jingir – Kwankwaso

Al’ummar Kano ba su tare da kalaman Sheikh Jingir – Kwankwaso

Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya ce kalaman da malamin addinin musulunci Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi na iya haifar da rarrabuwar kawuna a tsakanin al’ummar Najeriya.

A wata sanarwa da Kwankwaso ya wallafa a shafinsa na X, ya jaddada cewa al’ummar Kano ba su tare da irin waɗannan kalamai na yunƙurin rarraba kawuna ba

Ya ce ya damu matuƙa da kalaman da Sheikh Jingir ya yi a wani taro a Kano a ƙarshen mako.

A ƙarshen makon nan ne kafar sada zumunta da ma kafafen yada labarai suka ɗauki ɗimi da musayar yawu da cece-kuce kan kalaman da shugaban majalisar malamai ta ƙungiyar Izala, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi dangane da takarar Muslim-Muslim.

Kwankwaso wanda mataimakin ɗantakarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC Peter Obi ne, ya ce abin damuwa ne ganin irin waɗannan kalamai suna fitowa daga bakin malamin addinin da ke da matsayi da tasiri a tsakanin al’umma.

“Bai kamata mu yi amfani da muryarmu wajen faɗin kalaman da za su iya raunana haɗin kan ƙasarmu ba.”

Ya ce a wannan lokaci da Najeriya ke ciki, ya kamata a yi watsi da duk wasu kalaman da ka iya haifar da rashin haɗin kai.

Comments (0)
Add Comment