INEC Ta Kara Wa’adin Miƙa Sunayen Yan Takarar Gwamna da Majalisun Jihohi

INEC ta ƙara wa’adin miƙa sunayen ƴan takarar gwamna da majalisun jihohi

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya (INEC) ta tsawaita wa’adin da jam’iyyun siyasa za su shigar da sunayen ‘yan takararsu na zaɓen gwamna da na majalisun dokokin jihohi daga ranar 8 zuwa 11 ga Agustan 2026.

INEC ta ce ta ɗauki matakin ne bayan roƙon da jam’iyyun siyasa suka yi na ƙarin lokaci domin kammala aikin miƙa bayanan ‘yan takararsu.

Haka kuma, hukumar ta dakatar da rabon katin zaɓe na dindindin (PVC) a Jihar Osun gabanin zaɓen gwamna da za a gudanar ranar 15 ga Agusta.

INEC ta ƙara da cewa ta samar da sababbin katunan zaɓe ga wasu masu zaɓe a ƙananan hukumomin Odo-Otin da Ife Central bayan da wasu ɓata-gari suka sace katunan daga cibiyoyin rabonsu, tana mai jaddada cewa ba za a iya amfani da katunan da aka sace wajen kaɗa ƙuri’a ba.

Comments (0)
Add Comment