Jiragen Yaki Sun Tarwatsa ’Yan Bindiga A Kan Iyakar Kebbi da Zamfara

Jiragen yaki sun tarwatsa ’yan bindiga a kan iyakar Kebbi da Zamfara

Jiragen yakin sojojin Najeriya sun tarwatsa gungun wasu ’yan ta’adda a kan iyakar jihohin Zamfara da Kebbi.

Hadin gwiwar dakarun sojin kasa tare da ’yan sanda kwantar da tarzoma da kuma Rundunar Sojin Sama na Operation FANSAN YAMMA, sun ragargaji ’yan ta’addan ne bayan wata arangama mai zafi da wata babbar tawagar ’yan bindiga a kan iyakar jihohin biyu.

Rahotanni sun ce ’yan bindigar, kimanin mutum 240, sun gamu da gamonsu a hannun sojojin ne bayan sun fito ne daga yankin Sangeko Gap da ke Zamfara, inda suka nufi garin Makuku da ke Jihar Kebbi.

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa ’yan ta’addan suna kan babura, kuma sun rarraba kansu zuwa rukuni uku yayin da suke kutsa cikin yankin.

Wannan lamari ya tayar da hankulan mazauna ƙauyuka da ke kan iyakar, inda wasu suka fara barin gidajensu domin neman mafaka a wuraren da suka fi aminci.

A halin yanzu, jami’an tsaro suna ƙoƙarin dakile harin tare da haɗin gwiwar sojoji a ƙasa da kuma tallafin jiragen sama na Operation FANSAN YAMMA.

jami’an tsaro suna kokarin hana ’yan bindigar samun damar shiga ƙauyuka da kuma katse motsinsu a yankin iyakar.

Shigowar wannan babbar tawaga ta sake haifar da damuwa ga al’ummomin da ke kusa da wurin artabu.

An shawarci mazauna yankin da su kasance cikin shiri, su kuma bi umarnin jami’an tsaro yayin da aikin ya ke ci gaba.

Mataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar ta 8 ta Sojin Najeriya/Sector 2, Operation FANSAN YAMMA, Laftanar Kanar Olaniyi Osoba, ya shaida wa wakilinmu cewa aikin yana ci gaba, kuma za a fitar da ƙarin bayani bayan kammalawa.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da gudanar da ayyukan soja a fadin yankin Arewa maso Yamma domin tarwatsa sansanonin ’yan bindiga, ceto waɗanda aka yi garkuwa da su, da kuma dawo da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa.

Comments (0)
Add Comment