Amurka Za Ta Sanya Takunkumi Kan Gwamnonin Arewa 12, Alkalai Da Sarakunan Gargajiya Saboda Zargin Cin Zarafin Addini

Gwamnatin Amurka ta fara shirin sanya takunkumi kan gwamnoni, alkalai da sarakunan gargajiya 12 daga yankin Arewa saboda zargin goyon bayan wariyar addini da kuma kisan Kiristoci a Najeriya.

Rahoton Politics Nigeria ya ce wannan mataki yana cikin kudirin doka da Sanata Ted Cruz ya gabatar, wanda ke neman a sanya Najeriya cikin jerin kasashen da ke “Cin zarafin ’yancin addini”.

Jihohin da abin ya shafa sun haɗa da Zamfara, Kano, Sokoto, Katsina, Bauchi, Borno, Jigawa, Kebbi, Yobe, Kaduna, Niger,da Gombe. Idan kudirin ya wuce, takunkumin zai haɗa da hana visa, toshe kadarori da dakatar da tallafi daga Amurka a wadannan jihohin.

Gwamnatin Najeriya ta musanta zargin, tana mai cewa matsalar tsaro da ke yankin Arewa ba ta da alaka da addini, sai dai ta ta’addanci da satar shanu. Shugaba Bola Tinubu zai gana da tsohon shugaban Amurka Donald Trump domin tattauna batun da tabbatar da fahimtar juna tsakanin kasashen biyu.

Comments (0)
Add Comment