An ƙaddamar da shirin rigakafin cutar Polio a yankin tafkin Chadi

Ƙasashen Najeriya da Kamaru da Afirka ta tsakiya (CAR) da kuma Chadi da Nijar sun ƙaddamar da wani shirin rigakafin cutar Polio a yankin tafkin Chadi.

Shirin na sa ran yi wa yara aƙalla miliyan 83 rigakafin.

An ƙadamar da shirin ne domin kawar da nau’i na biyu na cutar Polio, wanda aka samu a ƙasashen Kamaru da Chadi da Nijar da kuma Najeriya.

Wani rahoto da aka fitar ya nuna cewa an samu yara jimilla 210 da suka kamu da cutar a ƙasashe huɗu, amma ba a samu ɓullar ta a Jamahuriyar Afirka ta tsakiya ba.

Comments (0)
Add Comment