An ba da rahoton cewa wasu ’yan daba sun kona masallatai da coci-coci a wurare da dama a arewaci da kudancin Habasha.
Kafin hakan dai, Tashin hankali ya barke bayan da aka kashe akalla musulmi 20 tare da jikkata wasu daruruwa, a lokacin da suke halartar jana’izar wani malami a ranar Talata a birnin Gonder da ke yankin Amhara.
Jami’in harkokin addinin musulunci na yankin ya shaidawa manema labarai cewa an kona masallatai hudu.
An kuma kona Majami’u uku a kudancin Habasha, kamar yadda shugaban hukumar gudanarwa na Cocin Orthodox a Silte ya tabbatar wa Manema labarai.
A wani abin da ake ganin tamkar ramuwar gayya ce ta tashin hankalin da aka yi a kwanakin baya.
Gwamnati ta ce an kama mutane 280 da ake zargi da hannu a tashin hankalin a birnin Gonder.