An ba da rahoton cewa wasu ’yan daba sun kona masallatai da coci-coci a wurare da dama a Arewaci da Kudancin Habasha

0 67

An ba da rahoton cewa wasu ’yan daba sun kona masallatai da coci-coci a wurare da dama a arewaci da kudancin Habasha.

Kafin hakan dai, Tashin hankali ya barke bayan da aka kashe akalla musulmi 20 tare da jikkata wasu daruruwa, a lokacin da suke halartar jana’izar wani malami a ranar Talata a birnin Gonder da ke yankin Amhara.

Jami’in harkokin addinin musulunci na yankin ya shaidawa manema labarai cewa an kona masallatai hudu.

An kuma kona Majami’u uku a kudancin Habasha, kamar yadda shugaban hukumar gudanarwa na Cocin Orthodox a Silte ya tabbatar wa Manema labarai.

A wani abin da ake ganin tamkar ramuwar gayya ce ta tashin hankalin da aka yi a kwanakin baya.

Gwamnati ta ce an kama mutane 280 da ake zargi da hannu a tashin hankalin a birnin Gonder.

Leave a Reply

%d bloggers like this: