Shugaba Buhari ya ce gwamnatinsa za ta cigaba da zage damtse wajen dawo da kayayyakin tarihi na Najeriya da aka sace

0 78

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatin tarayya za ta ci gaba da zage damtse wajen ganin an dawo da kayayyakin tarihi na Najeriya da aka sace daga kasashen waje, ciki har da Tagulla 1,130 mallakin masarautar Benin, wacca yanzu haka suke a gidajen tarihi na kasar Jamus.

Shugaban ya bayar da wannan tabbacin ne jiya a Abuja yayin da ya karbi bakuncin Oba na Benin, Oba Ewuare na II, tare da rakiyar mambobin kotun masarautar Benin da kwamitin amintattu na gidan adana kayan tarihi na Benin.

Mai Martaba Sarkin ya ziyarci fadar shugaban kasa ne domin mika godiyarsa ga shugaban kasar bisa dawo da wasu daga cikin kayan tarihin guda biyu, daga jami’ar Cambridge da ta Aberdeen da ke kasar Birtaniya bayan sacewa kimanin shekaru 125.

Da yake jawabi game da dawo da kayayyakin tarihi, shugaba Buhari ya bayyana jin dadinsa da yadda ya kawo farin jini da yabo ga kasar nan da tsohuwar masarautar Benin da kuma farin ciki ga Oba na Benin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: