Labarai

Rundunar Civil Defence za ta tura akalla jami’ai 565 domin tabbatar da bikin Idin karamar Sallah ta bana a jihar Yobe cikin koshin lafiya

Rundunar tsaron farin kaya ta kasa Civil Depense reshen jihar Yobe, ta ce za ta tura akalla jami’ai 565 domin tabbatar da bikin Idin karamar sallah ta bana a jihar cikin koshin lafiya.

Kwamandan rundunar jihar, Useni Navokhi, shine ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun rundunar, ASC Bala Garba a Damaturu.

Mista Navokhi ya ce jami’ain su za su kiyaye tare da bada tsaro a dukkanin filayen Idi a jihar kafin ranar Sallah da kuma ranar, don hana duk wani aiki marar kyau.

Ya kuma umurci dukkan Kwamandojin yanki da kuma jami’an dake kananan hukumomi17 na jihar, da su kasance masu jajircewa da tabbatar da tsaro wajen gudanar da ayyukansu.

Kwamandan ya kuma bukaci jama’a da su rika bayar da sahihan bayanai na mutanen da ake zargi cikin gaggawa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: