Duk wanda aka kama zai yaba wa aya zaki, gwamnatin Kaduna ba ta nada kwamitin yin sulhu da ‘Yan bindiga ba

Gwamnatin jihar Kaduna ta gargadi masu yayada cewa wai ta nada kwamitin yin sulhu da’ Yan bindiga a madadin gwamnatin a jihar da su shiga taitayin su tunda wuri ko kuma su yaba wa aya zaki.

A wata takarda da kwamishinan tsaron jihar, Samuel Aruwan ya fitar ranar Lahadi, gwamnatin jihar ta karyata wannan labari da ya karade shafukan jaridu da na sada zumunta a yanar gizo.

” An jawo hankalin gwamnatin Kaduna karkashin jagorancin gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, wai gwamnati ta nada kwamiti domin yin sulhu da ‘yan bindiga a jihar.

” Muna so mu tattabar wa mutane cewa wannan magana babu gaskiya a cikin sa, sannan kuma tuni har gwamnati ta dana tarkon kama duk wanda sune suka kirkiro wannan abu da kuma wadanda ke da hannu wajen kirkiro kwamitin karyar.

” Matsayar gwamnatin Kaduna kan ‘ Yan bindiga na nan daram, ba za ta yi sulhu da su ba. Duk wanda yake yin haka a madadin gwamnatin jihar, ya sani ba da dawun gwamnati yake yi ba, idan kuma aka kamashi ko shi waye, Kotu za ta raba su da gwamnati.

Idan ba a manta ba gwamnan jihar Kaduna El-Rufai, ya fadi ya kuma kara jaddadawa cewa gwamnatin sa ba za ta biya mudin fansar wani ga mahara. El-Rufai ya ce yin sulhu da mahara ba shi bane abin yi kuma gwamnatin sa ba za ta yi haka ba.

A ra’ayin gwanma El-Rufai, a bisu inda suke a ragargaje su shine kawai mafita, amma a rika bi ana dankara musu kudi na babu gaira babu dalili, zai basu karfin guiwar ci gaba da abinda suke yi ne.

Comments (0)
Add Comment