Gwamna Badaru Abubakar ya bukaci matasan Arewacin Najeriya su kwantar da hankulan su game da kisan Filato

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar na Jihar Jigawa ya bukaci matasan Arewacin Najeriya su kwantar da hankulan su domin Jami’an tsaro suyi aikin su wajen zakulo mutanen da sukayi kisa a jihar Plateau.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da Babban Mataimaki na Musamman ga Maigirma Gwamnan Jihar Jigawa a Sabbin Kafafen Sadarwa Auwal Danladi Sankara ya rabawa manema labarai a Dutse.

A cewarsa, gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ziyarci Gwamnan Jihar Plateau Simon Bako Lalong a birnin Jos domin jajanta masa.

An rawaito cewa kimanin Matafiya Musulmai 25 ne suka fito daga Jihar Bauchi zuwa jihar Ondo aka kashe su a jihar.

Kazalika, Gwamna Badaru Abubakar ya ce tuni Jami’an tsaro suka fara gudanar da bincike kan lamurin tare da kama wadanda ake zargin da kashe matafiyan.

Comments (0)
Add Comment