Kamfanonin kula da jirage sun dakatar da ayyuka ga Max Air kan bashin Naira biliyan 1

Matakin ya haddasa tsaikon zirga-zirgar jiragen cikin gida, yayin da Max Air ke fuskantar zargin rashin biyan kuɗaɗen ayyuka

Ƙungiyar Kamfanonin Kula da Ayyukan Jiragen Sama ta Najeriya (AGHAN) ta dakatar da ayyukan da take yi wa kamfanin jiragen sama na Max Air, bisa zargin rashin biyan bashin da ya kai kusan Naira biliyan 1.

Matakin ya janyo tsaiko ga wasu daga cikin zirga-zirgar jiragen cikin gida na kamfanin a faɗin ƙasar nan, lamarin da ya haifar da tangarɗa a harkokin sufurin jiragen sama.

Shugaban AGHAN, Olaniyi Adigun, ya ce sun ɗauki wannan mataki ne bayan kamfanin ya gaza amsa kiraye-kirayen da suka yi masa domin sasanta basussukan da ake bin sa.

A cewarsa, yayin da wasu kamfanonin jiragen sama da ake bin bashi suka fara tattaunawa da kamfanonin kula da jirage domin tsara yadda za su biya bashin, Max Air bai nuna wata niyya ta shiga irin wannan tattaunawa ba.

Ya ce matakin dakatar da ayyukan ya zama wajibi domin nuna wa sauran kamfanoni cewa ba za a ci gaba da ba da sabis ba tare da biyan kuɗin da ake binsu ba.

Sai dai ya bayyana cewa matakin ba zai shafi jigilar maniyyatan aikin Hajji ba, domin kuɗaɗen ayyukan da suka shafi jiragen Hajji ana biyansu ne kai tsaye ta hannun Hukumar Alhazai ta Ƙasa.

Rahotanni sun nuna cewa bashin da ake zargin Max Air na bi ya shafi manyan kamfanonin kula da jirage guda biyu, wato Skyway Aviation Handling Company Plc da Nigerian Aviation Handling Company Plc.

Tun da farko AGHAN ta yi barazanar dakatar da ayyuka ga kamfanonin jiragen sama da ke bin bashin kuɗaɗen ayyukan kula da jirage, amma ta ɗage matakin domin bai wa ɓangarorin damar sasanta matsalar.

Ƙungiyar ta ce ci gaba da rashin biyan kuɗaɗen ayyukan na jefa kamfanonin kula da jirage cikin matsin tattali, tare da barazana ga dorewar ayyukan da suke yi a fannin sufurin jiragen sama.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Max Air ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.

Comments (0)
Add Comment