Yadda Aka Yi Wa Mai Sharhi A Kafafen Sada Zumunta Kisan Gilla A Kano

Yadda aka yi wa mai sharhi a kafafen sada zumunta kisan gilla a Kano

An gano gawar wani fitaccen mai sharhi a kafafen sada zumunta, Ibrahim Khalil Dan Shagamu, mai shekaru 54, a gidansa da ke Gaida, a Ƙaramar Hukumar Kumbotso ta Jihar Kano.

’Yan uwansa sun ce wasu mutane da ba a san ko su waye ba sun shiga gidansa da ƙarfi, inda suka kashe shi ta hanyar yi .asa yankan rago.

Yar uwarsa, Aisha Muhammad Lawal, ta ce an sanar da su faruwar lamarin da misalin ƙarfe 12:30 na dare.

Ta ce ’yan sanda sun isa wajen, inda suka ɗauki gawarsa zuwa asibiti, daga bisani suka miƙa wa iyalinsa.

Ta ce an kama mutane biyu da ake zargi da hannu a kisan.

Marigayin ya rasu ya bar mata da ’ya’ya shida.

Iyalinsa sun ce ba sa zargin kowa a lamarin, amma sun buƙaci gwamnati ta tabbatar an yi adalci.

Ya taɓa kai ƙarar barazanar kashe shi
Kafin rasuwarsa, Dan Shagamu ya wallafa wani bidiyo a kafafen sada zumunta, inda ya bayyana cewa ana barazanar kashe shi.

Ya roƙi Gwamnan Kano, Sarkin Kano da ’yan sanda da su taimaka masa.

A lokacin ya zargi wasu maƙwabtansa da ’ya’yansu da ke yawan tsangwamarsa da kuma yi masa barazana.

Ya ce wasu yara sun taɓa jifan gidansa da duwatsu, suka lalata masa talabijin tare da taruwa a wajen gidansa suna zagi da yi masa barazana.

’Yan sanda sun kama mutum 2

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta tabbatar da kama mutum biyu da ake zargi da hannu a kisan.

Kakakin rundunar, CSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce waɗanda aka kama suna hannun ’yan sanda, yayin da ake ci gaba da bincike.

Ya ce bincike dai bai nuna cewa kisan na da alaƙa da ayyukan Dan Shagamu a kafafen sada zumunta ba, sai dai ana kallon lamarin a matsayin rikicin da ya samo asali daga hassada da ƙiyayya tsakaninsa da maƙwabtansa.

Amnesty ta buƙaci a gudanar da bincike
Ƙungiyar Amnesty International ta yi Allah-wadai da kisan, tare da neman a yi cikakken bincike.

Ƙungiyar ta ce dole ne a kama tare da gurfanar da duk waɗanda ke da hannu a kisan, tana mai cewa ya kamata a kare masu sukar gwamnati da sauran ƴan ƙasa masu bayyana ra’ayoyinsu, ba a kashe su ba.

Amnesty ta kuma nuna damuwa kan ƙaruwar kisa, barazana da tsoratarwa a Najeriya, musamman yayin da ƙasar ke tunkarar zaɓen 2027.

Comments (0)
Add Comment