Messi Ya Cimma Yarjejeniya Ta Sayen Kungiyar Eldense Ta Spain

Messi ya cimma yarjejeniya ta sayen ƙungiyar Eldense ta Spain

Fitaccen ɗan wasan Argentina, Lionel Messi, ya cimma yarjejeniya ta farko domin mallakar ƙungiyar CD Eldense, wadda ke buga gasar rukuni na biyu a Spain.

Rahotanni sun ce Messi na shirin mallakar kashi 100 cikin 100 na hannayen jarin ƙungiyar, bayan cimma matsaya da ƙungiyar masu zuba jari ta Colombia mai suna TH Soluciones Group S.A.S., wadda ta mallaki Eldense tun Oktoba 2025.

Sai dai har yanzu yarjejeniyar na buƙatar kammala wasu matakai na doka, ciki har da binciken harkokin kuɗi na ƙungiyar da amincewar Majalisar Wasanni ta Spain (CSD). Idan ta kammala, wannan zai zama ƙarin saka hannun jari na Messi a ƙwallon ƙafa bayan mallakar ƙungiyar UE Cornellà a farkon 2026.

Comments (0)
Add Comment