Wani mutum ya shiga hannu kan zargin kashe mahaifiyarsa a Osun
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Osun, ta kama wani mutum mai suna Taye Kasali, bisa zargin kashe mahaifiyarsa, Kudirat Kasali, sakamakon rikicin gona.
Kakakin rundunar, DSP Abiodun Ojelabi ne, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.
Ya ce lamarin ya faru ne a ranar 31 ga watan Agusta, lokacin da Kudirat da ɗanta Taye suka je gonarsu a yankin Bode-Osi.
A cewarsa, an samu taƙaddama a tsakaninsu a lokacin da suke cikin gonar.
’Yan uwan Kudirat sun kai rahoton ɓacewarta ofishin ’yan sanda na Bode-Osi bayan ba ta dawo daga gona ba.
’Yan sanda sun fara bincike, inda suka kama Taye a ranar 7 ga watan Satumba.
A cewar ’yan sandan, Taye bai musanta zargin ba.
Ya ce ya kashe mahaifiyarsa ne saboda tana kiransa da “mahaukaci” kuma tana ƙoƙarin sayar da gonar da ya yi iƙirarin cewa mallakinsa ce.
Taye, ya shaida wa jami’ai cewa ya yanke maƙogwaron mahaifiyarsa da adda, sannan ya birne gawarta a cikin gonar.
Bayan haka, ya jagoranci ’yan sanda zuwa wajen da ya birne gawar.
Rundunar ta kuma gano addar da ake zargin ya yi amfani da ita wajen aikata laifin a matsayin shaida.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, CP Ibrahim Zungura, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan lamarin kafin gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.