An yanke wa matar nan ‘yar kasar Australia da aka samu da laifin kashe iyalanta uku ta hanyar cin abinci mai guba hukuncin daurin rai da rai.
Alkalin da ya yanke hukuncin a Melbourne, ya ce babu wani sassauci da Erin Patterson za ta samu a hukuncin da aka yanke mata har nan da shekaru 33.
Ya ce babu wata nadama da matar ta nuna akan laifin da ta aikata, abin ta sani kawai shi ne ta san dalilin da ya sa ta aikata wannan laifi.
Wakiliyar BBC ta ce tsawon lokacin da aka kwashe ana mata shari’a ta kasance idonta a rufe inda take bude su ne idan alkali ya ce mata ta bude kuma babu wata alamar nadama a tare da ita.