Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta kama wasu mutum kunshin tabar wiwi da sholisho

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta kama wasu mutane bakwai lokacin da ta kai farmaki zuwa wajen aikata laifuka da maboyar batagari a kananan hukumomin Birninkudu da Gwaram.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Lawan Shiisu, ya tabbatar da kamen ga Kamfanin Dillancin Labarai na kasa a yau a Dutse.

Shiisu Adam ya ce uku daga cikin wadanda ake zargin, masu shekaru tsakanin 20 zuwa 28, an kama su ne a kauyen Babaldu da ke karamar hukumar Birninkudu, lokacin da tawagar ‘yan sanda da ke sintiri suka kai farmaki zuwa wajen aikata laifuka da maboyar batagari a garin.

Ya bayyana cewa an samu kunshi 85 na ganyen da ake zargin tabar wiwi ce, da kwayoyi guda 136, da sholisho ga 24, da kuma wuka guda daya a yayin farmakin.

Shiisu Adam ya kara da cewa ana cigaba da gudanar da bincike kafin a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu.

Comments (0)
Add Comment