Tsohon shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya kai wata ziyarar girmamawa ga tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a safiyar yau a birnin London.
koda yake ba’a bayyana dalilin ziyarar ba, sai dai abin da ya ja hankalin jama’a shi ne cewa yau ce ranar zagayowar haihuwar Abdulrasheed Bawa, inda ya cika shekara 45 da haihuwa.
A shekarar 2021, Bawa ya kafa tarihi a matsayin shugaban EFCC mafi kankantar shekaru da ya taba jagorantar hukumar tun kafuwarta, A lokacin, yana da shekaru 41 kacal.
Bugu da ƙari, shi ne mutum na farko da ba jami’in dan sanda ba da ya rike wannan mukami a tarihin hukumar.