APC Ta Ce Gwamnan Plateau Caleb Mutfwang Ya Sauya Sheƙa Daga PDP Zuwa APC

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta tabbatar da cewa Gwamnan Jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya fice daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa All Progressive Congress (APC).

A wata sanarwa da jam’iyyar ta fitar, APC ta ce Mutfwang ya kammala sauya sheƙarsa a hukumance, lamarin da, a cewar jam’iyyar, ya sa dukkan jihohin yankin Arewa ta Tsakiya (North Central) ke karkashin jagorancin APC.

Sai dai, har zuwa lokacin hada wannan rahoto, gwamnatin Jihar Plateau ko jam’iyyar PDP ba su fitar da wata sanarwa a hukumance don mayar da martani kan batun ba.

Comments (0)
Add Comment