Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Ganduje, ya jaddada cewa babu wani ɗan siyasa daga Kudancin Najeriya da ya fi Shugaba Bola Ahmed Tinubu dacewa da jagorantar ƙasar nan bayan shekarar 2027.
Ganduje ya bayyana hakan ne a Abuja yayin da yake karɓar baƙuncin wata tawaga ta shugabannin matasa daga Arewacin Najeriya, wakiltar dukkan jihohi 19 na Arewa.
Babu wani ɗan Kudu da ya fi Asiwaju Bola Ahmed Tinubu cancanta ya shugabanci Najeriya a 2027,” in ji Ganduje.
Ya gargaɗi masu sukar wannan ra’ayi da kada su ɗauka cewa masu zaɓe daga Arewa za su canza goyon bayansu zuwa wani ɗan takara a zaɓen shugaban ƙasa na gaba.
“Game da zaɓen 2027, duk waɗanda ke tunanin ko ke fata cewa Arewa za ta kaɗa ƙuri’a ga wani ɗan takara ba Asiwaju ba, suna yin babban kuskure,” ya yi gargaɗi.
A cewar Ganduje, Tinubu na da kwarewa da tarihin siyasa na musamman da ke bambanta shi da sauran ’yan siyasa, yana ƙara da cewa Najeriya ta yi sa’a samun shugaban ƙasa da rayuwarsa gaba ɗaya ta ginu a kan siyasa da gwagwarmayar dimokuraɗiyya.
“Wannan ne karo na farko da Najeriya ta yi sa’a ta samu shugaban ƙasa cikakken ɗan siyasa.
Tsohon Gwamnan Jihar Kano ya kuma tunatar da rawar da Tinubu ya taka a gwagwarmayar neman dimokuraɗiyya a Najeriya, yana mai jaddada irin sadaukarwar da ya yi a lokacin mulkin soja.
“A gaskiya, ya sha wahala; har ma ya tafi gudun hijira domin dimokuraɗiyya ta dore a Najeriya. Saboda haka, babu wanda ya fi Bola Ahmed Tinubu cancanta a sake zaɓa a 2027,” Ganduje ya ƙara da cewa.
Har ila yau, ya ambaci wata yarjejeniyar siyasa da aka cimma tun kafin zaɓen tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, wadda a cewarsa ta tanadi cewa mulki zai koma Kudancin ƙasa bayan shekaru takwas.
“Asiwaju bai kai shekaru huɗu a mulki ba tukuna, amma mun riga mun ga matakan da ya ɗauka da gyare-gyaren da ya aiwatar,” in ji Ganduje. “Gyare-gyaren da ya gabatar domin inganta ci gaban zamantakewa da tattalin arziƙin wannan ƙasa.”