Dalibai 50 da aka sace a jihar Neja sun tsere daga hannun masu garkuwa CAN

Akalla dalibai 50 daga cikin waɗanda aka sace daga makaranta St. Mary, dake Papiri, a Karamar Hukumar Agwara ta Jihar Neja, sun tsere daga hannun masu garkuwa da mutane.

’Yan bindiga sun kai hari makarantar ne da sanyin safiyar Juma’a, inda suka harbi mai gadin makarantar sannan suka yi awon gaba da fiye da dalibai 200, tare da ma’aikata 13 na koyarwa a makarantar.

A rahoton farko da shugaban Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) na Jihar Neja, Most Rev. Bulus Dauwa Yohanna — wanda shi ne mai mallakar makarantar — ya fitar, ya ce an sace dalibai 215 da ma’aikata 12.

Sai dai daga baya, a ranar Asabar, ya ce dalibai 88 ba a san inda suke ba.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka masa, Daniel Atori, ya fitar a safiyar Lahadi, Yohanna ya tabbatar da cewa dalibai 50 sun tsere daga hannun miyagun kuma sun dawo gida sun haɗu da iyayen da ‘yan uwa.

Yohanna ya bayyana cewa makarantar tana da firamare da sakandare, kuma tana da ɗalibai masu kwana da masu zuwa gida.

Comments (0)
Add Comment