Shugaban Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA), Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya, ya sake jaddada cewa dole ne a fara gwajin miyagun kwayoyi ga sabbin ‘yan yi wa ƙasa hidima (NYSC) a matsayin matakin kariya, ba hukunci ba.
Yayin wata ziyara da babban daraktan NYSC, Birgediya Janar Olakunle Nafiu ya kai hedkwatar NDLEA a Abuja, Marwa ya bayyana cewa wannan mataki zai taimaka wajen gano matsala tun kafin ta tsananta.
Ya ce kididdiga ta nuna cewa daya cikin bakwai na ‘yan Najeriya ‘yan tsakanin shekaru 15 zuwa 64 na amfani da miyagun kwayoyi, kuma babu wani yanki a kasar nan da matsalar ba ta shafa ba.
Marwa ya bukaci a kara hada kai da NYSC wajen fadada dakaru masu ilimi a bangaren lafiya da bayar da shawarar zuwa cibiyoyin jinya da hukumar ke da su, domin kara yaki da wannan annoba ta kwayoyi da ke lalata matasa.