EFCC bata kama tsohon Gwamnan jihar Kano ba, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso

Jagoran cibiyar sadarwa ta kungiyar Kwankwasiyya, Mallam Sunusi Bature Dawakin Tofa yace hukumar EFCC bata kama tsohon Gwamnan jihar Kano ba, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso kamar yadda ake yadawa a kafafen yada labarai.

Jagoran, cikin wata sanarwa, yace Kwankwaso ne da kansa ya ziyarci ofishin hukumar domin wanke kansa dangane da wasu zarge-zarge marasa tushe da ake tuhumarsa.

Yace tsohon Gwamnan ya ziyarci helkwatar hukumar domin bayar da bayaninsa dangane da zarge-zargen kuma ya gana da jami’an hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa na wasu awanni.

Sanarwa ta kara da cewa tsohon ministan tsaron ya bayyana zarge-zargen a matsayin bita da kullin siyasa.

Comments (0)
Add Comment