Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, na shirin komawa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ranar Litinin, 26 ga Janairu, 2026, kwanaki kaɗan bayan ya fice daga jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP).
An tabbatar da wannan shirin sauya sheƙa ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, daya fitar a ranar Lahadi.
A cewar sanarwar, Gwamna Yusuf ya bayyana cewa shawarar da ya yanke na komawa APC ta samo asali ne daga halin da ake ciki a fannin shugabanci, haɗin kan ƙasa da kuma ci gaba.
Gwamnan ya tunatar da cewa yana daga cikin farkon ’yan APC tun a shekarar 2014, lokacin da ya shiga jam’iyyar kuma ya zama ɗan takarar ta na kujerar Sanatan Kano ta Tsakiya, wadda daga baya ya miƙa wa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso domin kara haɗin kan jam’iyya.
Bayan shekaru na mu’amalar siyasa a ƙarƙashin jam’iyyu daban-daban, ciki har da zaman da ya yi a NNPP, Gwamna Yusuf ya ce APC ta kasance jam’iyyar da ya saba da ita kuma wadda ta fi tsari da dacewa wajen shugabanci na ci gaba.
Ya ce komawarsa jam’iyyar mai mulki za ta ƙarfafa haɗin kai tsakanin Jihar Kano da Gwamnatin Tarayya.
“Komawa APC zai ƙara bunƙasa haɗin gwiwa da Gwamnatin Tarayya, ya hanzar ta bunƙasar ababen more rayuwa, ya inganta haɗin kai a fannin tsaro, tare da ƙara inganta ayyukan gwamnati ga al’ummar Jihar Kano,” in ji gwamnan.
Ya ƙara da cewa wannan mataki zai taimaka wajen ƙarfafa kwanciyar hankalin siyasa da kuma inganta haɗin kai a cikin jihar.
Sanarwar ta bayyana cewa Gwamna Yusuf zai yi rajista a hukumance a matsayin ɗan APC a Kano ranar Litinin, tare da ’yan Majalissar Dokokin Jihar Kano 22, ’yan Majalissar Wakilai 8, da kuma shugabannin kananan hukumomi 44 na jihar.
Haka kuma ana sa ran zai ƙaddamar da shirin rajistar APC ta yanar gizo (e-registration) a Jihar Kano a ranar guda.