Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya bayyana damuwa bisa karuwar cin zarafin mata, musamman fyade a jihar, inda yayi alkawarin sanya dandaka a cikin sabuwar dokar cin zarafin bil’adama wacce ya sanyawa hannu kwanannan.
Bala Mohammed ya fadi haka lokacin da ya karbi bakuncin ministar harkokin mata da cigaban yara, Pauline Tallen, wacce ta kai masa ziyarar aiki jiya a gidan gwamnati dake Bauchi.
- Za’a farfado da ayyukan kungiyoyin taimakon kai da kai a jihar Jigawa
- Hukumar STOWA zata fara rangadi shiyoyin hukumar guda bakwai daga mako mai zuwa
- ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai mata biyu na kwalejin kimiyya da fasaha da ke Tsafe
- Hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya ta fara sayar da takardar sheda na shekarar 2024
- Najeriya kasa ce mai aminci ga masu saka hannun jari – Bola Tinubu
Gwamnan yace za a mayar da dokar cin zarafin bil’adama zuwa majalisar dokokin jihar, domin tabbatar da an gyare-gyare a inda aka samu sabani.
Tunda farko, a jawabinta, ministar harkokin mata da cigaban yara, Pauline Tallen, ta bayyana fyade a matsayin abinda yafi kisan kai muni.