Gwamnatin jihar Kano ta bayyana shirinta na daidaita farashin ruwan sha da ake siyarwa ga jama’a domin kawar da matsalar hauhawar farashin da ba shi da misali.
Kwamishinan ruwa na jihar, Umar Doguwa, ya ce an lura cewa masu sayar da ruwa na kara farashi a yadda suka ga dama, daga naira 100 da safe zuwa naira 200 da yamma ba tare da wani dalili ba.
Gwamnatin za ta sanya doka ta yadda idan jarkar ruwa tana naira 10 ne, ya zama haka a ko’ina, kuma za a haɗa da masu ruwan rijiyar burtsatse, da masu motocin ruwa da masu sayarwa a titi don samun daidaito.
Shugaban kungiyar direbobin ruwan tanki, Abdussalam Rimingado, ya yaba da matakin yana mai cewa zai taimaka wajen tsaftace kasuwarsu da rage wahalar da jama’a ke fuskanta wajen samun ruwan sha a farashi mai sauki.