Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da aikin gyaran na’urar tiransimita mai gajeren zango (shortwave) ta gidan rediyon Muryar Nijeriya (VON) mai ƙarfin kilowat 250 TX2 a tashar da ke unguwar Lugbe a Abuja.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, wanda Babban Sakatare a ma’aikatar, Mista Ogbodo Chinasa Nnam ya wakilta, shi ne ya bayyana hakan a bikin ƙaddamar wanda aka yi a jiya Talata a Abuja.
Idris ya bayyana wannan mataki a matsayin wani “muhimmin lokaci a tarihin Muryar Nijeriya, domin mun fara aikin farfaɗo da tasha mafi girma kuma mafi ƙarfi a nahiyar Afrika wadda yanzu ake sanya mata ingantattun na’urori na zamani da suka dace da fasahar zamani.”
Idris ya gode wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu bisa hangen nesan sa da jajircewar sa wajen zamanantar da kayan aikin yaɗa labarai a Nijeriya.
An kafa shi a cikin 1961 a matsayin sashen labaran ƙetare na gidan rediyon NBC, wato wanda ya zama FRCN daga bisani. Firayim Minista na lokacin, Alhaji Sa Abubakar Tafawa Balewa, shi ne ya ƙaddamar da shi.