Hukumar INEC zata fara baiwa fursunoni damar kada kuri’a a lokacin zabe

Hukumar zaɓen Nijeriya INEC ta ce za ta bai wa fursunoni damar kada kuri’a a lokacin zaɓe daga gidajen gyaran hali.

Shugaban hukumar, Mahmood Yakubu, ne ya bayyana hakan a ranar Juma’a yayin karɓar bakuncin babban kwanturolan hukumar gidajen gyaran hali ta ƙasa, Sylvester Nwakuche, a hedikwatar INEC da ke Abuja.

Yakubu ya tabbatar da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara, wanda ya bai wa fursunoni ‘yancin yin rajista da kada kuri’a a kowane zaɓe.

Comments (0)
Add Comment