Majalissar zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da fitar da kudi sama da naira miliyan 194 domin gudanar da karin ayyukan magance zaizayar kasa da ambaliyar ruwa a wajen da ake gina sabon asibitin kwararru na Kazaure.
Kwamishinan yada labarai matasa da wasanni na jiha Alhaji Bala Ibrahim Mamsa ya sanar da hakan bayan zaman majalisar da Gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya jagoranta.
- Airtel ta dakatar da bayar da bashin kati da data a Najeriya
- ’Yan adawa ba su isa su razanar da ni ba – Tinubu
- Sojoji sun kama masu satar man fetur a Legas, sun kama mutum 14
- Talauci ya ragu daga kaso 91 zuwa 41 a jihar Sokoto
- Bayan shekaru 12 da sace ɗaliban Chibok 272, har yanzu ba a san makomar 83 ba
Ibrahim Mamsa yayi bayanin cewa majalisar ta amince da karin ayyukan ne sakamakon rahotan data samu wanda ke nuni da cewar zaizayar kasa da ambaliyar ruwa na barazana ga aikin gina asibitin.
Kwamishinan ya cigaba da cewa tun farko an bada kwangilar aikin ne akan kudi naira biliyan dubu 1 da miliyan 893.