Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sanar da sabon tsari dangane da bayar da biza ba na ɗindindin ba ga ‘yan Najeriya

A wata sanarwa da ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja ya fitar a jiya Talata, an bayyana cewa wannan sabon tsari ya fara aiki nan take daga jiyan 8 ga Yuli, amma an jaddada cewa duk wata biza da aka bayar kafin wannan rana za ta ci gaba da aiki kamar yadda aka tsara tun farko.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sanar da sabon tsari dangane da bayar da biza ba na ɗindindin ba ga ‘yan Najeriya, inda mafi yawan irin waɗannan biza za su kasance biza guda ɗaya kacal da ingancin wata uku.

Ofishin ya ce wannan mataki na cikin tsarin da ake duba daidaiton manufofin bayar da biza a duniya, musamman don tabbatar da tsaro, da sahihancin takardun tafiye-tafiye, da kuma raba bayanan tsaro tsakanin ƙasashe.

Sai dai duk da wannan sabon shiri, Amurka ta jaddada cewa tana ci gaba da daraja dangantakar ta da Najeriya, tare da bayyana cewa tana aiki tare da hukumomin Najeriya don su kai matsayin da ake buƙata, tana kuma yabawa da gyare-gyaren da hukumomin shige da fice da tsaro ke yi domin bin ƙa’idojin da ake bukata a matakin ƙasa da ƙasa, tana mai roƙon ‘yan Najeriya su tabbatar da cewa takardunsu sahihai ne kuma suna bin ƙa’idojin biza.

Comments (0)
Add Comment