Masanin harkokin makamashi, Farfesa Wumi Iledare, ya bayyana cewa Majalisar Dattawa ta Ƙasa na ƙoƙarin zafafa da tayar da jijiyar wuya a kan binciken da take gudanarwa game da rashin daidaiton kudade a cikin bayanan kudin kamfanin NNPCL, wanda ya kai kimanin ₦210 tiriliyan.
A cewar Farfesa Iledare, wanda ya bayyana haka yayin wata hira da manema labarai a Abuja, ya ce yana da muhimmanci majalisa ta gudanar da bincikenta cikin ladabi da tsarin doka, ba tare da nuna alamar son zuciya ko ƙoƙarin janyo hankalin jama’a fiye da kima ba.
“Bincike dai abu ne da ya kamata a yi domin tabbatar da gaskiya, amma yadda ake tafiyar da shi yanzu yana ɗaukar salo na siyasa da tayar da ƙura, wanda zai iya hana samun sahihin sakamako,”
Majalisar Ƙasa, ta bakin Kwamitin Lissafin Kuɗi na Dattawa, ta fara bincike a kan wasu abubuwa da ake gani a matsayin rashin daidaito a cikin bayanan kudin NNPCL daga shekarar 2017 zuwa 2023. Binciken ya haɗa da tambaya kan kudaden da aka rubuta a matsayin “kudaden da ake bin su” da kuma “kudaden da za a karɓa” da suka kai jimillar ₦210 tiriliyan.
Majalisar ta bai wa NNPCL wa’adin kwanaki 10 domin gabatar da bayani, inda daga baya aka ba da ƙarin makonni uku bayan bayyanar Shugaban Kamfanin, Injiniya Bayo Ojulari, a gaban kwamitin.
Sai dai Farfesa Iledare ya ce, irin wannan gaggawa da rashin hakuri da majalisar ke nunawa yana iya ɓata manufar gaskiya da bin doka.
“Idan ana son gaskiya da adalci, kamata ya yi a ba kamfanin damar gabatar da bayanai cikin tsari, ba wai a rinka tayar da kura a kafafen yada labarai ba,”
Ya ƙara da cewa ya kamata a bar hukumomin da suka dace su gudanar da bincike cikin kwarewa da kwararan hujjoji, maimakon yayata shi a matsayin wani salon shari’a ta kafar watsa labarai.